
Wani Bidiyon Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana inda aka jishi yana wata barazana.
An ji Wike na barazanar ne a wajan wani taron siyasa a jiharsa.
Ya bayyana cewa mutum kada ya zo ya kawo musu abinda ba shi kenan ba a jihar Rivers.
Wike bai fadi da wanda yake ba inda yace mutum ya tambayi abinda ya faru da wadanda suka yi yunkurin yiwa jihar Rivers kutse a baya.
saidai wasu sun ce da sakataren Jam’iyyar APC yake inda wasu kuma ke cewa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yake.