
A ranar Juma’a ne wani Al’amari mai kama da wasan kwaikwayo ya faru a fadar Sarkin Bauchi, inda aka zargi mataimakin gwamnan jihar Auwal Jatau da Zabgawa ministan harkokin kasashen Waje Yusuf Maitama Tuggar Mari a Sa’ilin da wata hatsaniya mai zafi ta barke Tsakannin Ministan Da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad.
Lamarin ya faru ne a lokacin da ake bikin nada tsohon gwamnan jihar Bauchi, Barrista Mohammed Abdullahi Abubakar, a matsayin Makama Babba na Masarautar Bauchi, wanda ya yi daidai da daurin auren diyarsa, Khadija Mohammed.
Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan yan siyasa da suka hada da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima,da gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya da dai sauransu.
A cewar shaidun gani da ido, rikicin ya samo asali ne bayan da rahotanni suka ce ministan harkokin wajen kasar ya yi kalaman batanci ga gwamnatin Kauran Bauchi Bala Mohammed,kalaman da ake zargin sune suka Fusata mataimakin gwamnan.
“Kalaman Ministan sun Fusata Mataimakin gwamnan, inda ba don gaggawar shiga Tsakanni da mataimakin shugaban kasa Shettima yayi ba, da tuni lamarin ya kazance” wata majiya ta shaida wa wakilinmu.
Tun farko dai Tuggar ya zargi gwamnan da yin amfani da sauye-sauyen harajin shugaban kasa Bola Tinubu wajen kaddamar da muradin sa na shugaban kasa a 2027.
A cikin watan Janairu a gidan talabijin na Channels TV’s, Tuggar ya ce: “Gwamna Bala Mohammed ya nuna a fili cewa ba shi da wata manufa ta gaskiya.