
Tauraron fina-finan Hausa da Tiktok, Baana ya fito ya kira sunan matar Rarara, Aishatulhumaira ya bata hauri kan kalaman da yayi akanta.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya wallafa yanzu inda yace yana neman afuwar taurin kan da yawa iyayensa.
Yace abinda ya fada na cewa Rarara na kai matar tasa wajan manya suna kamata, ta yi hakuri yayi kuskure.
Hakan na zuwane bayan da A’ishatulhumaira ta kai karar Baana gaban DSS inda tace ya yi mata da mijinta Qazafi.