Friday, December 26
Shadow

Da Duminsa: Cutar Shanyewar Rabin jiki ta kama Ministan kudin Najeriya an garzaya dashi asibitin kasar waje

Rahotanni sun bayyana cewa, cutar Shanyewar rabin jiki ta kama Ministan Kudi, Wale Edun inda aka garzaya dashi zuwa asibitin kasar waje

Sahara reporters ta bayyana cewa, lamarin yayi tsanani anma yana samun kulawa ta musamman a asibitin da aka kaishi.

Rahotan yace ministan yana aiki da yawa ba tare da hutu ko cin abinci yanda ya kamata ba wanda ake ganin hakan ya taimaka sosai wajan rashin lafiyar tasa.

Rahoton yace Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Cordoso ne aka wakilta ya maye gurbin ministan zuwa wani babban taron kudi da za’a yi a kasashen waje.

Rahoton yace ko da ministan ya warke da wuya ya koma bakin aikinsa inda rahotanni suka ce tuni shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara neman wanda zai nada a matsayin sabon Ministan kudin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Mazan Najeriya kuwa Allah ku daina Aikomin da sakon cewa kuna sona, Bature nake son in aura, Farar Fata, wanda zai kaini kasarsu>>Inji Wannan baiwar Allahn

rahoton yace fadar shugaban kasa ta tabbatar da rashin lafiyar ministan kudin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *