Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Dangote zai sayar da wani sashe na matatar mansa

Rahotanni sun bayyana cewa, Attajiri, Dangote zai sayar da wani kaso tsakanin kaso 5 zuwa 10 na matatar mansa a kasuwar hannun jarin Najeriya.

Dangote ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a kafar  S&P Global ranar 20 ga watan October inda yace zai yi hakanne kamar yanda yawa kamfanoninsa na sukari dana Siminti.

Dangote yace baya son rike fiye da kaso 65 zuwa 70 cikin 100 na hannun jarin matatar man.

Yace a hankali a hankali zai rika sayar da hannun jarin matatar ya danganta ga yanda mutane ke son saye ko kuma yanayin kasuwa.

Hakanan Dangote yace yana son kara yawan man fetur din da suke tacewa duk rana zuwa ganga Miliyan 1.4 a kowace rana.

Karanta Wannan  Kungiyar Malaman Jami'a ta ASUU ta sanar da janye yajin aiki

Idan hakan ta tabbata, matatar man Dangote zata zama ta daya a Duniya wajan yawan fitar da man fetur inda zata zarta ta kasar India dake Jamnagar, India wadda a halin yanzu itace ke tace man fetur mafi yawa a Duniya na ganga Miliyan 1.36 duk rana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *