
Rahotanni daga kafar peoplesgazette sun bayyana cewa, Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya gana da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a Saudiyya.
Kafar tace wata majiya ta gaya mata cewa, Gwamna Sule yawa Atiku Alkawarin zai bashi kudi yayi yakin neman zabe sannan kuma ya bashi tabbacin shine zai ci jihar Nasarawa a zaben 2027.
Kafar tace a yanzu Atiki bashi da isassun kudin da zai yi yakin neman zabe bayan da a baya yayi takara har sau 4 ba tare da nasara ba.
Sannan a zamanin Mulkin Buhari an durkusar da kamfaninsa na Intel.