
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya musanta rahoton dake cewa, yana shirin komawa jam’iyyar gamayyar ‘yan Hamayya ta ADC.
Gwamnan yace Rahoton karyane bashi da tushe ballantana makama.
Gwamnan Zulum yace shi dan APC ne kuma yanawa jam’iyyar Biyayya sannan kuma yace mutanen jihar Borno ne a gabanshi.
Gwamnan yace yana kira ga mutane da su rika tantance labari kamin su yadashi.