Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Ina cikin tsama mai wuya, ana barazanar rabani da kujerara>>Inji Shugaban NNPCL, Bayo Ojulari

Shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari ya bayyana cewa, Rayuwarsa data sauran ma’aikatan kamfanin na cikin hadari.

Yace ana barazanar saukeshi daga kan mukaminsa, inda yace laifinsa kawai shine kyaran da ya kawo a harkar mai a kasarnan kamar yanda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bashi umarni.

Ya bayyana hakane a Abuja yayin da kungiyar ma’aikatan man, PENGASSAN ta kai masa ziyara bisa jagorancin shugabanta, Comrade Festus Osifo.

Yace suna kokarin ganin an gyara matatun man fetur din Najeriya sun dawo aiki yanda ya kamata.

Karanta Wannan  Bayan Allah sai Tinubu a gurina, dan ko iyalina, da mahaifana basu kaimun Tinubu ba>>Inji Ministan Ayyuka, David Umahi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *