
Rahotanni daga Kano na cewa, Jam’iyyar NNPP a jihar ta kori shugabanta, Hashim Suleman Dungurawa.
NNPP tace ta kori Hashim Suleman Dungurawa ne saboda zargin kawo rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar NNPP a Mazabar Gargari dake karamar hukumar Dawakin Tofa, Shuaibu Hassan ne ya bayyana haka ga BBChausa.
Korar shugaban NNPP din ta fara ne daga ranar 30 ga watan Disamba.
Hakan na zuwane a yayin da ake rade-radin Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf zai koma jam’iyyar APC.