
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Ingila na shirin dawowa da Najeriya Dala Miliyan $9.5 da ake zargin tsohon shugaban soja, Marigayi, Janar Sani Abacha da sacewa.
A baya dai an dawowa da Najeriya irin wadannan kudade da yawa.
Saidai ‘yan kasa na korafin cewa wasu ne ke sake sace kudin dan ba’a ganin abinda ake yi dasu.