Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Kungiyar Malaman Jami’a ta ASUU ta tsunduma yajin aikin gargadi na sati biyu

Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya Asuu ta bai wa mambobinta umarnin fara yajin aiki daga gobe Litinin na tsawon mako biyu.

Academic Staff Union of Universities (Asuu) ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa’adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata.

Shugaban Asuu Farfesa Chris Piwuna ya faɗa yayin taron manema labarai a Abuja cewa matakin ya zama dole “saboda gazawar gwamnatin wajen biyan buƙatunmu”.

Karanta Wannan  Jimullar Naira Tiriliyan 2.23 'yan Najeriya suka biya tsageran daji a matsayin kudin fhansa>>Inji Gwamnati

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *