Sunday, March 23
Shadow

Tonon Silili: Dama can Sanata Akpabio da Natasha Akpoti sun san juna kamin ta zama sanata>>Inji Daya daga cikin sanatocin

Sanata me wakiltar Birnin Tarayya, Ireti Kingibe ta bayyana cewa dama can sanata Natasha Akpoti da kakakin majalisar, Godswill Akpabio sun san juna kuma akwai wani abu a tsakaninsu kamin ta zama sanata.

Ta bayyana hakane a yayin da sanata Natasha Akpoti ta fito ta zargi kakakin majalisar da cewa ya nemeta da lalata ne ta ki shiyasa ya canja mata gurin zama a majalisar kuma yake dakile kudirorin da take kawowa.

Sanata Ireti Kingibe ta bayyana cewa, ba Sanata Natasha Akpoti kadai bace aka canjawa wajan zama a ranar ba.

Ta jawo hankalin cewa hakan tsari ne na majalisar wanda kuma duk dan majalisar ya kamata yana girmama hakan.

Karanta Wannan  Ku daina Tsinuwa da zagi ga shuwagabanni, Addu'a ya kamata ku rika musu>>Sarkin Musulmi ga 'yan Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *