
Rahotanni sun bayyana cewa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya saye kusan dukkan fom din takara na jam’iyyar PRP a jihar Kano.
Hakan ya fito ne daga bakin shugaban jam’iyyar na jihar, Abdulkadir Musa Guza.
Yace sun je taron jam’iyyarsu a Kaduna inda suke shirin fara sayar da fom din takara sai aka ce masa wani ya saye duka fom din takarar.
Yace da ya matsa da tambaya an bayyana masa cewa Kwankwaso ne kuma an sayar masa ne saboda ana tattaunawa dashi zai koma jam’iyyar ta PRP.
Yace amma sun ga alama Kwankwaso bashi da niyyar komawa jam’iyyar yaudararsu yayi.
Yace dan haka suke shirin makashi a kotu kobya dawo musu da fom dinsu.