
Rahotanni daga jihar Rivers sun bayyana cewa, Majalisar Jihar ta fara shirin tsige gwamnan jihar, Simi Fubara.
An ga kakakin majalisar a wani Bidiyo daya watsu sosai a kafafen sada zumunta yana cewa ‘yan majalisar 26 sun sakawa takardar neman tsige Fubara hannu.
Majalisar tace tana zargin Gwamna Fubara da karya dokar kundin tsarin Mulki.
Kuma sun ce zasu aika masa da takarda kan hakan.
Hakanan majalisar ta kuma ce ta fara shirin tsige mataimakin Gwamnan na jihar Rivers, Ngozi Nma Odu.
Majalisar ta kuma ce ta dakatar da shirin Gwamna Fubara na kai mata kasafin kudin shekarar 2026.