
Rahotannin da muke samu na cewa, matatar man fetur ta Dangote ta sake rage farashin man fetur dinta.
Matatar tace a yanzu a Legas za’a rika sayar da man fetur din akan Naira N875 kan kowace lita sai kuma a kudu maso yamma za’a rika sayar da man nasu akan Naira N885 kowace lita.
A Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya kuwa za’a rika sayar da man fetur din ne akan Naira N895 duk lita.
Hakanan tace a jihohin Kudu maso gabas da kudu maso kudu kuma za’a rika sayen man fetur din akan Naira N905 kowace lita.
Matatar tace za’a samu man fetur din a wannan farashin a gidajen mai abokan hildarsu, wanda suka hada da MRS, AP, Heyden, Optima, TechnOil, da Hyde.