Friday, December 12
Shadow

Da Duminsa: Matatar man Dangote ta sake rage farashin Man fetur

Rahotannin da muke samu na cewa, matatar man fetur ta Dangote ta sake rage farashin man fetur dinta.

Matatar tace a yanzu a Legas za’a rika sayar da man fetur din akan Naira N875 kan kowace lita sai kuma a kudu maso yamma za’a rika sayar da man nasu akan Naira N885 kowace lita.

A Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya kuwa za’a rika sayar da man fetur din ne akan Naira N895 duk lita.

Hakanan tace a jihohin Kudu maso gabas da kudu maso kudu kuma za’a rika sayen man fetur din akan Naira N905 kowace lita.

Matatar tace za’a samu man fetur din a wannan farashin a gidajen mai abokan hildarsu, wanda suka hada da MRS, AP, Heyden, Optima, TechnOil, da Hyde.

Karanta Wannan  An soki Tinubu saboda kaddamar da titin Legas zuw Calabar da ba'a kammala ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *