
A karshe dai, Mijin sanata Sanata Natasha Akpoti, Chief Emmanuel Uduaghan wanda basarakene a Warri ya yi magana kan abinda ya faru tsakanin matarsa da Sanata Akpabio.
Chief Emmanuel Uduaghan ya bayyana cewa matarsa ta kawo mai korafi akan neman yin lalata da ita da sanata Akpabio ke son yi.
Yace a matsayinsa na basarake sannan kuma Sanata Akpabio abokinsa ne, bai nemi rikici ba, ya je ya samu sanata Akpabio inda suka yi magana ta hankali ya gargadeshi cewa ya daina neman yin lalata da matarsa.
Chief Emmanuel Uduaghan ya kara da cewa amma abin mamaki shine matarsa ta ci gaba da kawo mai kuka akan Sanata Akpabio.
Yace ya yadda da matarsa tana kare kanta bata cin amanarsa kuma tana da gaskiya.
Yace mutane su daina biyewa duk kokarin da ake na kawar da hankali daga kan maganar.
Yace yanzu dai a jira sakamakon binciken da ake akan lamarin ya fito.