
Tsohon hadimin shugaban kasa a zamanin mulkin tsohon ahugaban kasa, Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya tabbatar da cewa, Sanata Natasha Akpoti ta taba masa kazafin cewa yana son yin lalata da ita.
Yace akwai wata kawar Sanata Natasha Akpoti wadda taso ya nemeta ya kiya.
Yace daga nan ne kawai sai ya ji Natasha Akpoti wadda a wancan karin ba sanata bace tace wai ya nemi yin lalata da ita a ranar da tsohon shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta ya kawo ziyara Na3.
Yace abin mamaki shine a wancan lokacin ba ya ma Najeriya, shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya aikashi ya wakilceshi a kasat Amurka kuma har ya dauki hotuna da wakilan kasar Amurka da yawa.
Yace bayan da ya dawo ya hadu da zargin da Natasha ke masa, sai ya gabatar da hujjojinsa wanda da taga ba zata yi nasara ba, sai ta goge duka zarge-zargen da take masa a kafafen sada zumunta.
Yace saidai a yayin da yake tunanin matakin da zai dauka akanta, sai wani babban mutum da yake ganin girmansa ya kirashi ya bashi baki inda aka sasantasu.
Yace abinda ya faru tsakaninsa da Sanata Natasha Akpoti kenan amma bai san komai ba game da zargin da takewa Sanata Godswill Akpabio ba saboda baya wajan.
Yace kafafen watsa labarai da yawa nata kiransa dan yayi hira dasu akan lamarin amma gashinan abinda ya sani kenan game da sanata Natasha Akpoti.