
Matatar man fetur din Dangote ta sanar da cewa ta dawo ta ci gaba da sayar da man fetur da kudin Naira
Hakan na zuwane kasa da awanni 24 bayan da matatar tace ta dakatar da sayar da man fetur din da kudin Naira saboda man data tanada dan sayarwa da kudin Naira ya kare
Saidai a sabuwar sanarwar, Matatar Dangote tace ta dawo sayar da man fetur din da kudin Naira bayan shiga tsakani da shugaban kwamitin sayar da man fetur da kudin Naira, Dr. Zacch Adedeji yayi.
Matatar tace yanzu duk masu sayen man zasu iya saya da kudin Naira kuma zata kai musu kyauta.