Friday, July 17
Shadow

Da Duminsa: Mun dawo mun ci gaba da sayar da man fetur da kudin Naira>>Inji Matatar man Dangote, kasa da awanni 24 bayan da tace ta dakatar da sayar da man da kudin Naira

Matatar man fetur din Dangote ta sanar da cewa ta dawo ta ci gaba da sayar da man fetur da kudin Naira

Hakan na zuwane kasa da awanni 24 bayan da matatar tace ta dakatar da sayar da man fetur din da kudin Naira saboda man data tanada dan sayarwa da kudin Naira ya kare

Saidai a sabuwar sanarwar, Matatar Dangote tace ta dawo sayar da man fetur din da kudin Naira bayan shiga tsakani da shugaban kwamitin sayar da man fetur da kudin Naira, Dr. Zacch Adedeji yayi.

Matatar tace yanzu duk masu sayen man zasu iya saya da kudin Naira kuma zata kai musu kyauta.

Karanta Wannan  Na yi aiki da mata kyawawa masu yawa babu wadda ta taba cewa na nemeta sai Sanata Natasha Akpoti, dadin abin ba ni kadai ta taba kalawa sharri ba>>Sanata Godswill Akpabio

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *