
Ministan Tsaro, Muhammad Badaru ya bayyana goyon bayansa ga Matashin soja da ya tare Ministan Abuja, Nyesom Wike ya hanashi shiga wani fili a Abujan.
Minista Badaru yace suna goyon bayan abinda Sojan yayi kuma sun jinjina masa sannan zasu bashi kariya saboda yana bakin aikinsa ne.
Badaru yace zasu ci gaba da baiwa kowane soja Kariya da goyon baya muddin ya tsaya tsayin daka a bakin aikinsa.
Hakan na zuwane bayan da a wajan rikicin ma sai da Wike ya kira shugaban sojoji, CDS.