Friday, December 19
Shadow

Da Duminsa: Rahotanni na cewa sojan da ya shirya jhuyin mulki a kasar Benin Republic ya samu tserewa zuwa kasar Nijar, inda aka bashi mafakar siyasa acan

Rahotanni sun bayyana cewa, sojan da ya jagoranci juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar Benin Republic, Pascal Tigri yanzu haka yana zaune a kasar Nijar.

Rahoton yace Pascal Tigri ya samu mafakar siyasa a kasar ta Nijar inda yanzu haka yake zaune a wani gidan gwamnati dake kusa da fadar shugaban kasar Nijar.

Rahoton yace yanzu haka ana zargin kasar ta Nijar da hannu ko da ba kai tsaye bane a yunkurin juyin Mulkin.

Pascal Tigri da farko ya tsallaka zuwa kasar Togo ne inda daga nan ya hau jirgi zuwa Burkina Faso. Daga baya kuma ya sake hawa jirgi zuwa kasar Nijar.

Karanta Wannan  Mulkin Tinubu ya saka 'yan Najeriya cikin matsananciyar Wahala>>Obasanjo

Najeriya dai ta taimakawa kasar ta Benin Republic aka murkushe yunkurin juyin mulkin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *