
Rahotanni na ta yawo a kafafen sada zumunta inda ake yada cewa wasu matasa sun tare Tauraron fina-finan Hausa, Musa Mai Sana’a inda suka masa na jaki.
Shafin @kafinhausa dake X ya wallafa cewa, lamarin ya farune a Sharada dake Kano.
Mai Sana’a dai bai tabbatar da hakan da kansa ba, sannan babu wata kafa data kawo labarin, saidai labarin ya dauki hankula a kafafen sada zumunta inda mutane ke ta bayyana ra’ayoyinsu akai.