Thursday, May 14
Shadow

Ashe Tsugune bata kare ba, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana wata Mugunta da Gwamnati ta shirya masa dan tursasashi ya amince da bukatun Gwamnatin

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi zargin cewa, Gwamnati na son kama yayansa, Bashir El-Rufai dan a tursasashi ya amince da bukatun Gwamnatin.

Yace dalili ma kenan da yasa suka ce babban yayan nasu ya tsaya a birnin Cairo na kasar Egypt kada ya dawo Najeriya dan kar a kamashi.

Yace yanzu haka yana can.

ElRufai ya bayyana hakane a wajan zaman makokin mahaifiyar sa data rasu inda yakewa mutane godiya da irin aoyayyar da suka nuna musu.

Karanta Wannan  Maganar Mhuzghunawa Kiristoci a Najeriya karyace>>Inji Most Rev. Matthew Kukah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *