Saturday, April 11
Shadow

Da Duminsa: Sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC inda wani babban mutum shima ya maka su David Mark da Aregbesola a kotu yace ba halastattun shugabannin jam’iyyar bane

Dan majalisar wakilai, Leke Abejide wanda dan jam’iyyar ADC ne ya maka shuwagabannin jam’iyyar na riko David Mark, da Rauf Aregbesola a kotu inda yace kotu ta saukesu.

Hakan na zuwane a yayin da ake tsaka da fama da rikicin Nafiu Bala.

Ya shigar da karar ne a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja inda kotun ta tsayar da ranar 13 ga watan Afrilu dan yanke hukunci.

Jam’iyyar ADC na fuskantar kalubale kala-kala inda take zargin hannun APC a lamarin.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Tinubu Ya Aika Da Ƙudirin Biyan Mafi Karancin Albashi na Dubu N70,000 Ga NASS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *