
shahararren malaminnan na jihar Filato, Abubakar Abdullahi, wanda shine Imam na kauyen Nghar a Barkin Ladi jihar Filato ya rigamu gidan gaskiya.
Malamin shine wanda ya baiwa Kiristoci 262 kariya a masallaci da gidansa wanda dalilin hakan ya samu yabo da kyautuka a ciki da wajan Najeriya.
Dansa, Saleh Abubakar ne ya tabbatar da rasuwarsa ga gidan jaridar Daily Trust inda yace mahaifin nasu ya rasu ne a daren Alhamis.