
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya aikewa da majalisar Dattijai da bukatar su amince masa ya aika da sojoji kasar Benin Republic.
Kakakin Majalisar Dattijai Godswill Akpabio ya karanta wasikar da shugaba Tinubun ya aikawa majalisar.
Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da shugaba Tinubu ya aike da sojoji kasar ta Benin Republic suka hana juyin Mulki da sojojin kasar suka so yi.