
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya baiwa kowacce daga cikin ‘yan mata ‘yan Kwalon Najeriya na kungiyar super Falcons Dala $100,000.
Wannan kudi na daidai da kwatankwacin Naira Miliyan 152,000,000
Hakanan kowacce cikin ‘yan matan an bata kyautar girmamawa ta OON.
Hakanan kungiyar Gwamnonin Najeriya ta baiwa kowanne daga cikin ‘yan matan Naira Miliyan 10.