
Rahotanni daga fadar shugaban kasa na cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince ko ya saka hannu kan kudirin dokar saka Harajin kaso 15 cikin 100 akan man fetur da gas da ake shigowa dasu Najeriya.
Sakataren shugaban kasar, Damilotun Aderemi ne ya dauki takardar kudirin dokar inda ya kaiwa hukumomin da lamarin ya shafa dan a fara zartas da wannan doka.
Ana tsammanin wannan sabuwar dokar haraji zata kara farashin man fetur da akalla N0.99, kamar yanda The Cable ta ruwaito.