
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Najeriya a yau, Litinin bayan kwashe kwanaki 19 a Turai yana hutawa.
Dama dazu da rana fadar shugaban kasar tace yau zai dawo Najeriya.
Da farko dai an bayyana cewa sati biyu shugaban kasar zai yi amma daga baya sai gasho ya wuce hakan, wanda lamarin ya fara saka ‘yan Najeriya cikin damuwa.