Wednesday, November 19
Shadow

Ji yanda aka yi daurin auren dan ministan kudi ba tare da kowa ya sani ba saboda yace bai son Almubazzaranci musamman saboda halin da ‘yan Najeriya ke ciki

An daura auren dan ministan Kudi Wale Edun, me suna Mr. Tobi Edun a asirce ba tare da kowa ya sani ba.

Daurin auren ya samu halartar manyan mutane ma’aikatan gwamnati na ‘yan kasuwa amma ba’a yi Sharholiya ba.

Ministan kudin ne ya bukaci kada a yi almubazzaranci wajan bikin dan nasa.

Inda ake tsammanin ya dauki wannan mataki ne musamman saboda halin matsin da mafi yawan ‘yan Najeriya ke ciki, kamar yadda wata majiya a kusa dashi ta gayawa jaridar Vanguard.

Karanta Wannan  Yayin da suka rasa yanda zasu yi, kasar Nijar ta roki Najeriya ta taimaka mata da man fetur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *