
Rahotanni da Hutudole ke samu na cewa, Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya kara aure.
Rahotannin sun ce Adam A. Zango ya auri Salamatu wadda aka fi sani da Maimuna Musa ta Garwashi.
Sannan kuma itace ta fito Zaituna a Labarina.
Hutudole ya samu labari cewa an daura aurenne a ranar Lahadi, 17 ga watan Augusta.
Tuni dai ‘yan Uwa da abokan arziki suka fara taya su Murna.