Tuesday, August 25
Shadow

Duk da Hukumar Hisbah ta Kano tace ta je gidan yarin Goron Dutse ta ga ba gaskiya a zargin Luwadi da ake da yara, Saidai da yawa sun ce basu yadda da binciken na Hisbah ba, ciki kuwa hadda tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad

A jiyane Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da cewa ta je gidan gyara hali dake Goron Dutse inda aka yi zargin cewa ana luwadi da matasa da ake tsare dasu dan ta yi bincike.

Hukumar tace ta kammala binciken ta kuma ta gano cewa babu kanshin Gasol a zargin.

Saidai duk da haka wasu sun ce basu gamsu da binciken Hisbah ba, kamata yayi a samu dan jarida wanda bashi da alaka da gwamnati watau me zaman kansa yayi wannan bincike.

Wasu sun ce shin a yayin binciken da Hisbah ta yi an cire wandon yaran an ga yanayin lafiyar duburarsu, kuma an kaiwa likita ya dubasu?

Karanta Wannan  Najeriya ta zo ta biyu a yawan mutane matalauta a Duniya

Cikin masu irin wannan ra’ayi hadda Malam Bashir Ahmad wanda tsohon hadimin shugaban kasa ne.

Ya bayar da shawarar a baiwa dan jarida irin su jafar jafar damar zuwa wannan gidan yarin dan yin binciken kwakwaf

Karanta Wannan  Shugaban Jami'ar Tarayya Dake Lafia Kenan, AbdulRahman Yake Sanya Hannu A Jikin Rigunan Daliban Da Suka Kammala Karatu A Jami'ar, Inda Ya Hore Su Da Su Kasance Masu Da'a A Yayin Bukukuwan Kammala Karatun

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *