Wednesday, January 15
Shadow

Da Duminsa: Tinubu ya ba da umarnin sakin yaran da aka gurfanar a kotu kan zanga-zanga

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin sakin dukkan ƙananan yaran da aka kama da zargin cin amanar ƙasa sakamakon shiga zanga-zanga kan tsadar rayuwa.

Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya ce an kuma kafa wani kwamati da zai bincika yadda aka kama su da sauran lamurransu.

“Shugaban ƙasa ya ce a sake su kuma a sadar da su ga iyayensu,” in ji ministan lokacin da yake magana manema labarai a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Bayanan sun fito ne jim kaɗan bayan kammala rantsar da sababbin ministoci bakwai da Shugaba Tinubu ya naɗa a fadarsa a yau Litinin.

Kwamatin da zai yi aikin zai kasance ƙarƙshin ma’aikatar agaji da rage talauci, in ji ministan.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Tinubu Ya Aika Da Ƙudirin Biyan Mafi Karancin Albashi na Dubu N70,000 Ga NASS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *