
Rahotanni sun bayyana cewa, Tsohon Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano ya rasu a Asibitin kasar Ingila.
Rahoton yace ya rasu ne bayan yayi fama da cutar zuciya da kuma cutar mafitsara.
Wasu na kusa dashi sun tabbatar da rasuwar tashi inda suka ce ya dade yana fama da cutar amma kuma ta zo mai ne yanzu farat daya.