
Tsohon Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya yi karin haske game da rashin lafiyar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Bashir Ahmad yace a yayin da labarai ke ta yawo cewa, Shugaba Buhari bashi da lafiya, ya zama dole su fito su fayyace gaskiya.
Yace da gaskene Tsohon shugaban bashi da lafiya yana can kasar ingila yana jinya.
Yace suna godiya da nuna damuwa da mutane suka yi kuma suna mai fatan samun sauki.