Wednesday, November 19
Shadow

Saika fice mana daga jam’iyya tun da ka shiga gayyar su Atiku>>Labour Party ga Peter Obi

Ɓangaren Julius Abure na Jam’iyyar Labour (LP) ya ba Peter Obi wa’adin sa’o’i 48 ya yi murabus daga jam’iyyar saboda alakarsa da jam’iyyar haɗaka ta ADC da David Mark ke jagoranta.

Mai magana da yawun ɓangaren, Obiora Ifoh, a wata sanarwar da ya fitar ya ce jam’iyyar ba za ta yarda Obi ya haɗe da wata jam’iyya ba yayin da yake memba a Labour Party.

Sanarwar ta ce jam’iyyar ba ta goyon bayan mutane masu manufofi biyu ko masu yaudara, kuma duk wanda ke son ya goyi bayan jam;iyyar ADC ya yi murabus cikin sa’o’i 48.

Ɓabgaren Abure ɗin ta ce waɗanda ke cikin jam’iyyar haɗaka ‘yan siyasa ne masu son dawowa mulki ta kowanne hali.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda Aka warce wayar wannan Faston a kan Titin Birnin Landan yayin da yake daukar kansa hoton Bidiyo yana addu'a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *