
Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya musanta rahoton dake cewa ba zai tsaya takarar shugaban kasa ba a shekarar 2027.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakane ta bakin dan uwansa, Azibaola Robert inda yace Jonathan bai ce zai tsaya takarar shugaban kasa ba ko ba zai tsaya ba.
Hakan na zuwane yayin da PDP ke cewa tana son tsayar da ko dai Goodluck Jonathan ko Peter Obi takarar shugaban kasa a 2027.
Rahotanni sun ce tuni Goodluck Jonathan ya fara tuntubar manyan mutane a kasarnan kan tsayawa takarar shugaban kasar.