
Rahotanni sun ce ministan Abuja Nyesom Wike ya fadi abinda bai kamata ba akan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Ana ganin Wike a matsayin na hannun damar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu wanda ke abinda ya ga dama a gwamnatin Tinubu ba tare da an taka masa burki ba.
A kwanannan aka ruwaito cewa Wike ya baiwa ‘ya’yansa biyu filaye masu yawa a Abuja.
Hakanan kuma ya baiwa iyayensa da ‘yan uwa filayen.
A wani sabon labari da jaridar Peoplesgazette ta ruwaito, tace Wike yace babu abinda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai masa.
Sannan babu wani alkalin da ya isa ya daureshi a Najeriya.
Hakan na zuwane bayan da ake kira ga shugabab kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dauki mataki akan yanda Wike ke abinda ya ga dama a Gwamnatinsa.