
Rahotanni sun bayyana cewa, wutar Lantarkin Najeriya ta lalace.
Hukumar wutar lantarki ta Abuja ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa data wallafa a X.
Rahotanni sun ce wannan shine karo na 5 da aka samu wannan matsalar a shekarar 2025.
Da yawa dai sun bayyana cewa hakan abin kunyane.