Monday, August 10
Shadow

Ni ne gatan ‘yan Najeriya, Duk wani da zai zo ya ce muku zau kayar dani zabe a 2027 kada ku saurareshi>>Shugaba Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa ce gatan ‘yan Najeriya inda yace kada su saurari masu cewa zasu kayar dashi zabe a 2027.

Shugaban yace ‘yan adawar dake hada kai da zummar kayar dashi zabe ‘yan gudun hijirar siyasa ne.

Shugaban ya bayyana hakane ranar Laraba a yayin ziyarar da ya kai jihar Nasarawa ta kwana daya.

Ya yabawa gwamnan jihar, Abdullahi Sule kan aikin da yakewa mutanen jiharsa inda yace zai tallafa masa da dukkan wani aikin ci gaba da zai kawo.

Karanta Wannan  Sabuwar Baraka ta kunno kai a jam'iyyar ADC, Ana zargin Atiku da saye duk wani me fada aji a jam'iyyar da kudi, Peter Obi ya koka da cewa an mayar dashi saniyar ware

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *