Rahotanni sun bayyana cewa, wutar Lantarkin Najeriya ta sake lalacewa a Yau Alhamis, 7/11/2024.
Hutudole ya samu rahoton cewa wutar lantarkin ta lalace ne da misalin karfe 11:20am na yau Alhamis.
Hukumar Nigeria National Grid ce ta tabbatar da hakan
Wannan ne karo na biyu da wutar ta lalace a cikin satin da muke sannan karo na 12 a cikin wannan shekarar da muke ciki.