
Rahotanni daga Kaduna na cewa ‘yansandan jihar sun gano wani bam da aka ajiyeshi a Bola a jihar.
Kakakin ‘Yansandan jihar, Mansir Hassan ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Yace an gano bam dinne a cikin wasu karikitai irin na masu jari bola a wani kanfanin sarrafa kayan bolar dake unguwar Kudenden.
Yace Bom din na cikin karikitan bola ne da aka dauko daga Borno zuwa Kaduna. Yace tuni ‘yansanda na musamman da suka iya kwance bom suka je wajan.
Yace bayan bincike an tabbatar da cewa, bam ne wanda bai tashi ba a cikin karikitan.
sannan an gano jarin makamai da suka hada da Bindiga da albarusai.
Yace an kulle kamfanin har sai an kammala kawar da kayan makaman.