Wednesday, April 29
Shadow

Kamar Dai BUA Shima Dangote ya sha Alwashin karya farashin Shinkafa

Attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote ya sha Alwashin karya farashin Shinkafa inda yace zai kafa kamfanin shinkafar a jihar Naija.

Hakan na zuwane kwanaki bayan da BUA ya sha Alwashin karya farashin shinkafar.

Babbar me baiwa shugaban kamfanin na Dangote shawara Fatima Abdurrahman ce ta bayyana haka inda tace aina gina kamfanin shinkafar ne a Wushishi.

Tace shirin gina kamfanin yana karkashin hadaka ne da Gwamnatin jihar Naija ke yi da kamfanoni masu zaman kansu.

Karanta Wannan  Bayan da mahaifin Bilyaminu ya fito ya ce ya yafewa Maryam Sanda kuma shine ma yayi kokarin ganin Shugaba Tinubu ya yafe mata, Wani dan Uwan Biliyaminun ya fito yace bayan rasuwar Biliyaminu, Mahaifin ya hanasu sakat akan Gado, Aka bashi Miliyan 5 amma yace bai yadda ba, ya je kotu saida aka bashi Miliyan 10 daga cikin kudin gadon

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *