
Rahotanni sun bayyana cewa, ‘Yansanda a babban birnin tarayya, Abuja sun kama dan fafutuka kuma me rajin kare hakin bil’dama, Omoyele Sowore.
An kamashi ne a yayin da yake fitowa daga cikin babbar kotun tarayya dake Abuja inda akewa Nnamdi Kanu shari’a.
Rahoton yace ‘Yansandan sun saka Sowore a gaba yayin da yake fitowa daga Kotun inda suka ce su wuce office.
Bayan da aka yi tirka-tirka Sowore dai ya yadda an tafi dashi.
Wani na kusa da Sowore yace dama can ‘yansandan sun gayyaceshi amma Azarbabin sune yasa suka zo kamashi.