
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, biyo bayan shigar hadakar jam’iyyun Adawa jam’iyyar ADC, shuwagabannin jam’iyyar duk sun ajiye mukamansu.
Lamarin ya farune a Shehu Musa Yar’Adua Centre dake Abuja.
Shugaban jam’iyyar Ralph Nwosu, ya tabbatar da hakan inda yace sun sauka ne dan yiwa shugabancin jam’iyyar garambawul.
Bayan saukarsu, an bayyana David Mark a matsayin sabon shugaban jam’iyyar sannan Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam’iyyar na riko.