Wednesday, November 19
Shadow

Facebook da Instagram na barazanar daina aiki a Najeriya saboda Harajin da Gwamnatin Tinubu ke saka mai yayi yawa

Kamfanin Meta iyayen Facebook da Instagram na barazanar ficewa daga Najeriya saboda yawan dokokin da gwamnatin tarayya ke gindaya musu.

Hakanan dayan dalilin da yasa kamfanin ke son ficewa daga Najeriya hadda harajin da ake kaka ba musu wanda suka ce yayi yawa.

Gwamnatin Najeriya ta maka kamfanin META a kotu akan zarge-zarge daban-daban inda take neman kamfanin ya biyata diyyar Dala Miliyan $290m, META sun shiga kotu amma basu yi nasara ba.

Kamfanin na Meta dai shine kuma ke da manhajar WhatsApp amma bai bayyanata cikin wanda zai kulle ba.

Kotun dai ta baiwa kamfanin nan da zuwa watan Yuni ya biya harajin da aka kakaba masa.

Karanta Wannan  Daya daga cikin matan da mutuminnan na kasar Equatorial Guinea yayi lalata dasu kuma Bidiyon lalatar ya bayyana ta kàshè kanta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *