
Rahotanni daga kasar Spain na cewa kasar ta bi sahun kasar Afrika ta Kudu wajan kai karar kasar Israyla kotun Duniya saboda zargin kisan kiyashi da Israyla kewa Falasdinawa.
Kasar Sifaniya dai ta dade tana kira ga kasashen Turawa da su kakabawa kasar Israyla takunkumi saboda kisan da takewa falasdinawa.
A kwanannan ne dai Birnin Barcelona na kasar ya yanke dukkan wata hulda da kasar Israela saboda kisan da sukewa Falasdiynawa.
Kasar Afrika ta kudu itace kasa ta Farko a Duniya data fara kalubalantar kasar Israela saboda kisan da takewa Falasdiynawa.