
Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya karyata rade-radin dake yawo cewa ya so ya sake zama shugaban Najeriya a karo na 3.
Obasanjo ya bayyana hakane a wajan wani taro kan Dimokradiyya da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya shirya.
Yace babu wanda zai iya cewa ya kirashi ya gaya mai cewa yana son zarcewa a karo na 3 akan mulki.
Yace neman a yafewa Najeriya bashin da ake binta da yayi a zamanin mulkinsa, yafi neman zama shugaban kasa a karo na 3 wahala.