
Daliban jami’o’in Federal University Kashere, Gombe dana jami’ar BUK, Kano Kiristoci sun koka da cewa, akwai masallatai da yawa a wadannan jami’o’in amma an hanasu gina coci ko guda daya.
Daya daga cikin daliban na Kashere ne ya fito yake zanga-zanga shi kadai inda yace suna bukatar Coci a jami’ar.
Wani kirista ta bayyana cewa abin haushin shine jihar Gombe da yawan musulmai da kirista daidai suke watau 50/50 amma irin wannan abin na faruwa.
Wannan zanga-zanga da dalibin yayi tasa shima wani dalibin jami’ar BUK Kano ya bayyana cewa suna hakan take, akwai masallatai a BUK amma su ba’a basu damar gina coci ba.